ilimi
Satar Ɗalibai: Hukumar tsaro ta Civil Defence ta tura jami’ai mata gadin makarantu
Hukumar tsaro ta civil defence ta tura da jami’anta mata don gadin makarantu a faɗin ƙasar nan baki ɗaya.
Shugaban hukumar, Ahmed Audi, shine ya ba da wannan umarni yayin zantawa da manema labarai a jiya laraba.
Ya ce an ɗau wannan mataki ne don kare lafiyar ɗalibai da malamai a makarantu da ke Najeriya.
‘‘Yanzu haka jami’an mu mata za su fara gudanar da wani atisaye tare da ɗaukar horo na wata ɗaya kafin su fara aikin nasu na ba da tsaro a makarantun ƙasar nan’’ inji Ahmed Audi.
‘‘Wannan mataki dai ya dace da umarnin da ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ya bayar a kwanakin baya.’’ A cewar sa.
You must be logged in to post a comment Login