Manyan Labarai
Satar yaran Kano da munafurcin kafafan yada labarai
A ranar jumaar da ta gabata ce rundunar yansanda ta jahar Kano tayi holen wasu mutane da suka sace kananan yara ‘’yan asalin jahar Kano zuwa jahar Anambra tare da sayar da su a garin Onitsha.
Rahotanni sun nuna cewa ba’a nan kawai ta tsaya ba, bayan satar yaran an canja musu addini daga na musulunci zuwa kiristanci, tare da mayar da su bayi.
Tun shekarar 2014 ne dai al’ummun wasu yankuna dake nan Kano da suka hada da unguwar Hotoro da Yankaba da Sauna da Kawaji da Dakata anan Kano suka rika korafin cewa ana sace musu yara kanana .
Satar yara kananan ya tayar wa da iyaye da dama hankali inda wasu daga cikin iyayan suka shiga bakin cikin rabuwa da ‘yayan nasu sakamakon sace su da aka yi a tsawon shekara biyar.
An dade ana tafka mahawara tsakanin al’umma daban daban anan Kano a game da dalilin da yasa ake satar yara a Kanana kuma ba tare da an gansu ba.
Ko a kwanakin baya sai da aka cafke wani dan kabilar Igbo a tashar motar sabongari da ake kira da a turance luxurious Bus station ya sace wani yaro a yankin unguwar Yankaba zai yi kudancin Najeriya da shi domin aikata ita wannan mummunar adawa ta sayar da yaran Kano.
Cafke wannan dan kabila ta Igbo shi ya saka rundunar ‘’Yanasandan jahar Kano karkashin tsarin nan na operation puff Adder suka shiga bibiyar wannan lamari har aka zo ga matakin da ake ciki na cafke masu satar yaran Kano da sayar da su da kuma canja musu Addini a yankin na kudu maso gabashin Najeriya.
Amma abun tambaya anan shi ne ,lokacin da labaran sace yaran suka yadu a kafafan yada labarai irin su jaridun Daily Nigeria , wasu daga cikin jaridun kasar nan basu mayar da hankali akan labaran da ya fito daga jahar ta Kano ba ,na sace yaran da mayar da su wani addini da ba nasu ba.
A lokacin da jaridun kudu suke bawa labarai da basu taka kara sun karya muhimmanci ba, da sauran al’amura na yau da kullum , sai ga shi labarin na yaran Kano bai zama labara mai muhimmanci ga jaridun na kudancin kasar nan ba.
A farkon shekarar 2016 ne dai wani dan asalin jahar Kano mai suna Yunusa Yellow aka zarge shi da tahowa da wata yarinya daga jahar Bayelsa mai suna Ese Oruru da aurar da ita har da zargin canja mata addini duk da zargin da aka yi na cewa ya aureta.
A wannan lokaci jaridun kudancin kasar nan sun yi nisa wajen ganin an kwatowa wannan yarinya ‘’yar asalin jahar Bayelsa Ese Oruru hakkin ta na ganin cewa ta samu yanci daga hannun matashi dan asalin karamar hukumar Kura.
Yunusa Yellow ta kai ga an gabatar da shi a babbar kotun tarayya dake Yenagoa babban birnin jahar Bayelsa.
Bayan nan jaridu irin su jaridar Sun, da sauran su, sun bibiyi labarin na Ese Oruru har zuwa garin na su domin bin bahasi akan abun da ya faru tsakanin Ese Oruru da Yunusa Yellow dan asalin karamar hukumar Kura.
Kungiyoyin Musulmi da dama da sauran kungiyoyi da na malamai sun yi shiru, banda kungiyar Muslims Right Concern wato MURIC da suka fitar da bayanai na tir da abunda ya faru na satar yaran na Jahar Kano.
Ko ina kungiyar hana fataucin yara da ta NAPTIP take, na gano matsalar da ake ciki a jahar Kano na sace yaran garin.
Ya kamata ace tuntuni Gwamnatin jahar Kano ta binciki abubuwan dake faruwa a wannan tashar ta Sabongari da ake amfani da ita, na diban yaran Kano domin mayar da su wani addini da ba nasu ba, kuma a matsayin su na kananan yara da aka keta musu hakki.