Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Saura ƙiris na fice daga PDP – Kwankwaso

Published

on

A ranar Laraba mai zuwa ne jagoran ɗarikar Kwankwasiyya zai fice daga jam’iyyar PDP zuwa NNPP.

Wata majiya mai ƙarfi daga jam’iyyar PDP ta tabbatarwa da Freedom Radio cewa Rabi’u Musa Kwankwaso ya kammala shirin sa tsaf domin ficewa daga jam’iyyar.

Tuni dai dama ake ta raɗe-raɗin cewa Kwankwason zai fice daga jam’iyyar zuwa mai kayan marmari ta NNPP.

Ko a yau Litinin 28 Maris, 2022 wata sanarwa da Salisu Muhammad Kosawa ya fitar ta sanar da cewa “Mai girma Jagora, Sen. Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso, yana gayyatar kafatannin Jagorori, shugabanni, ƴan Kwankwasiyya, da dukkanin jama’a zuwa taron kasa na Jam’iyyar NNPP da zai gudana a filin polo dake Gwarinpa Abuja, ranar Laraba 30/3/2022 da misalin karfe 10 na safe”.

Abin da ya sanya na fice daga PDP – Abba Gida-gida

Mun kaɗu da ficewar Abba Gida-gida – PDP

Wannan dai ya ƙara tabbatar da shirin ficewar Kwankwaso daga jam’iyyar PDP, kwana guda bayan da tsohon ɗan takarar gwamna a jam’iyyar ta PDP Abba Kabir Yusuf ya fice daga cikin ta zuwa NNPP.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!