Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sauya sheka ba zai hana mu bincikar ‘yan siyasar da ake zargi ba-EFCC

Published

on

Hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa ta’annati EFCC ta ce ‘yan siyasa da ke sauya sheka daga jam’iyyar su zuwa wata, ba shi ne zai hana hukumar bincikar su ba.

Mukaddashin shugaban hukumar na kasa Ibrahim Magu ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi a yayin taron editoci yau a Lagos, tare da cewa hukumar zata kara kaimi a yakin da take yi da cin hanci da rashawa.

Da yake mayar da martani game d zarge-zargen da ake cewa jam’iyya mai mulki ta APC na na sanya baki ga al’amuran hukumar, Ibrahim Magu ya bayyana cewa babu wani umarni da ya taba samu kan cewa EFCC ta dakatar da wani bincike ko kuma kai sumame.

A cewar Ibrahim Magu kasancewar babban zaben shekarar badi na gabatowa, dole hukumar ta EFCC ta kara zage dantse wajen yakar masu satar dukiyar kasa.

Shugaban hukumar ta EFCC yace akwai bukatar kafafen yada labarai su bayar da gudun mowar su wajen yakar cin haci da rashawa, ta hanyar bankado wadanda suke boye dukiyar da suka sace.

Ibrahim Magu ya kara da cewa hukumar EFCC ta sanya hannu kan yarjejeniyar aikin hadin gwiwa da kasashen Mauritius da kuma hadaddiyar Daular Larabawa cikin kudirin ta na kwato dukiyar kasar nan da aka sace aka kuma boye su a wasu kasashen.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!