Labarai
SERAP ta bukaci Shugaba Tinubu ya binciki yadda gwamnoni ke kashe kuɗaɗen tsaro

Kungiyar SERAP mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam da tabbatar da adalci a shugabanci a ayyukan gwamnati, ta bukaci Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da ya kafa kwamitin bincike domin tantance yadda gwamnonin jihohi ke kashe kuɗaɗen tsaro tun daga watan Mayu 2015 zuwa yanzu.
SERAP ta bayyana cewa akwai buƙatar gwamnati ta fito fili ta fayyace yadda ake batar da waɗannan kuɗaɗen da aka ware don sha’anin tsaro, tare da ɗaukar mataki kan duk wanda aka samu da hannu a aikata almundahana ko amfani da su ba bisa ka’ida ba.
Kungiyar ta yi gargadin cewa ɓoye gaskiyar yadda ake kashe makudan kuɗaɗen tsaro na iya haifar da gibin amincewa tsakanin al’umma da shugabanni, lamarin da ka iya jefa tsarin mulkin dimokuraɗiyya cikin hatsari.
You must be logged in to post a comment Login