Labarai
SERAP ta gurfanar da shugabannin majalisun tarayya a kotu

Kungiyar SERAP ta gurfanar da da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, kotu saboda kin bincikar zargin cewa ‘yan majalisa suna biyan har Naira miliyan uku domin gabatar da kudiri ko koke a majalisar.
Karar ta biyo bayan wani faifan bidiyo da dan majalisar wakilai daga jihar Jigawa, Ibrahim Auyo, ya yada inda ya ce ana karɓar tsakanin Naira miliyan 1 zuwa 3 domin a gabatar da kudiri ko koke a majalisar.
SERAP ta nemi kotu ta tilasta wa Akpabio da Abbas su mika lamarin ga hukumomin yaki da cin hanci don bincike da gurfanarwa, tare da daukar matakan kare Ibrahim Auyo da ya fallasa zargin.
Kungiyar ta ce wannan zargi babban cin amanar jama’a ne da ya sabawa rantsuwar kama aiki, tana mai jaddada cewa bai kamata cin hanci ya zama sharadi wajen gudanar da ayyukan majalisa ba.
You must be logged in to post a comment Login