Labarai
SERAP ta maka CBN a kotu kan rashin bada bayanan kudaden da aka tura wa kananan hukumomi

Kungiyar rajin tabbatar da adalci da daidato da yaki da cin hanci da rashawa SERAP ta yi karar babban bankin kasa CBN kan rashin bada cikakkun bayanan kudaden da aka biya kai tsaye ga kananan hukumomi 774 na kasar nan, ciki har da kudaden da aka aike wa kowace karamar hukuma.
Mataimakin shugaban kungiyar ta SERAP, Kolawole Oluwadare, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa daya fitar a yau Lahadi.
Ya ce karar kungiyar ta biyo bayan wani hukunci da kotun koli ta yanke a watan Yuli, inda ta ce dole ne a biya kason kudaden da aka ware daga asusun tarayya da CBN kai tsaye ga kananan hukumomin da aka yi zabe, kuma babu wani gwamna da ke da ikon rikewa, sarrafawa ko kuma yin amfani da kudaden da aka tanadar wa kananan hukumomin.
A cikin karar da ta shigar a ranar Juma’ar da ta gabata a babbar kotun tarayya da ke jihar Legas, SERAP na nemi kotun da ta umarci bankin na CBN ya bayyana bayanan duk wasu kudaden da aka biya kananan hukumomin 774 ciki har da kudaden da aka aika wa kowace karamar hukuma tun bayan hukuncin kotun koli.
You must be logged in to post a comment Login