Labarai
Kotu ta dage Shari’ar Kananan Hukumomin Kano

Babbar kotun tarayya mai lamba uku karkashin jagorancin mai shari’a Simon Amobeda, ta sanya ranar 26 ga watan gobe na Mayu domin ci gaba da shari’ar da wasu jagororin jam’iyyar APC suka shigar, ta nema hana babban Bankin kasa CBN, sakar wa kananan hukumomin jihar Kano 44 kudaden su kai tsaye.
A zaman kotun na yau Litinin, kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi da takwararta ta Malaman makarantu da kungiyar ma’aikatan lafiya ne suka bukaci shiga cikin shari’ar.
Tun da farko kotun ta yi hukuncin rushe shugabannin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC, tare da hana su gudanar da zaben kananan hukumomi da aka yi a watan Oktoban bara.
Amma ita kotun ta yi hukuncin cewar kada CBN din da kuma hukumar rabon albarkatun kasa su rike kudaden.
You must be logged in to post a comment Login