Labarai
Shari’ar Zaɓe: Alƙalai sun zauna don fara gabatar da shari’a
Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta shirya tsaf domin fara karanta hukuncin shari’ar gwamnan Kano da kuma bangaren jamiyyar APC.
Tun da fari dai gwamna Abba Kabir Yusuf shi ne ya shigar da ƙara, inda yake ƙalubalantar hukuncin kotun sauraran zabe wadda aka gudanar a kano.
Sai dai a yau ne kotun ta sanya domin yanke hukunci, wanda a halin yanzu kowane ɓangare ya halarci zaman.
A ɓangaren gwamnati mai ci ta NNPP kwamishinoni da dama sun halarci Kotun ciki har da sakataren gwamnati da shugaban jam’iyyar na Kano Hashim Dungurawa da na Abuja Dauda Yusuf.
Haka kuma a bangaren APC akwai ƙaramar ministar Abuja Dr. Mariya Bunkure da Rabiu Sulaiman Bichi da Aminu Dabo da sakataren jam’iyyar Zakari Sarina da Mutari Ishak da kakakin jamiyyar APC Ahmda Aruwa da kuma dumbin magoya bayansu.
A daidai wannan lokaci ana jiran shigowar Alƙalan da zasu gudanar da shari’ar.
You must be logged in to post a comment Login