Labarai
Shekarar 2026 za ta bude sabon babi na karuwar tattalin arziki mai karfi- Shugaba Tinubu

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa shekarar 2026 za ta bude sabon babi na karuwar tattalin arziki mai karfi, inda gwamnatin sa za ta kara rage hauhawar farashi, ta karfafa ajiyar kudaden waje.
A sakon sabuwar shekara da ya aikewa ’yan kasa, Shugaba Tinubu ya ce yana da kwarin gwiwa cewa hadin kan al’umma zai sa shekarar ta zama mafi alheri ga kasa da ’yan cikinta. Ya bayyana cewa a 2025, gwamnatinsa ta aiwatar da manyan gyare-gyaren tattalin arziki, ta sake daidaita harkokin kudi, kuma ta samu ci gaba.
Tinubu ya ce duk da kalubalen tattalin arzikin duniya,kasar nan ta samu gagarumar nasara, inda ake sa ran ma’auni GDP wanda yake auna karfin tattalin arzikin kasa zai haura kashi 4 cikin 100. Ya kara da cewa an samu daidaiton canjin kudade, tare da saukar hauhawar farashi zuwa kasa da kashi 15 cikin 100.
Ya jaddada cewa a 2026, gwamnati za ta kara rage hauhawar farashi tare da tabbatar da cewa amfanin gyare-gyaren tattalin arziki ya isa ga kowane gida a Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login