Labarai
Shettima ya dawo bayan kammala taron MDD karo na 80

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya dawo gida Najeriya bayan kammala babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 da aka gudanar a birnin New York tare da kai wata ziyarar aiki a ƙasar Jamus, da ya sauka a babban birnin tarayya Abuja.
A yayin zaman na mako guda na hulɗar ƙasashen duniya, Shettima ya gabatar da jawabin ƙasa na Shugaba Bola Tinubu inda ya yi kira ga cikakkun sauye-sauye a Majalisar Ɗinkin Duniya.
Haka kuma Shettima, ya jagoranci kare ikon Afirka kan albarkatun ma’adananta da aka ƙiyasta darajarsu a dala biliyan 700 tare da ƙarfafa hulɗa ta dabarun cigaba da Birtaniya da Gidauniyar Gates, da sauran manyan masu ruwa da tsaki a duniya.
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma tabbatar wa al’ummar Najeriya mazauna ƙasashen ketare cewa gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da ganawa da su a harkokin gudanarwarta.
You must be logged in to post a comment Login