Rahotonni
Shigo-shigo ba zurfi aikin gwamnati ga ‘dan jarida – Ja’afar Ja’afar
Dakataccen mai taimakawa gwamnan Kano kan kafafen yaɗa labarai Salihu Tanko Yakasai ya miƙa saƙon godiyarsa ga waɗanda suka aike masa da saƙonni da kiran waya na jaje kan dakatarwar da gwamna ya yi masa a cikin wani saƙo da ya fitar a shafinsa na Twitter.
A ranar Lahadi ne gwamnan Kano ya dakatar da Yakasai daga muƙaminsa, bayan da ya wallafa wani saƙo a shafin Twitter da ya danganta shugaban ƙasa Buhari da “mara tausayi”.
Har yanzu al’umma na ci gaba da bayyana mabanbantan ra’ayoyi kan dakatarwar da aka yi masa.
Mawallafin jaridar Intanet ta Daily Nigerian Ja’afar Ja’afar ya shaida wa Freedom Radio cewa dama aikin gwamnati ga Ɗan Jarida kamar shigo-shigo ba zurfi ne.
Ya ce kamata ya yi mutum ya lura kwarai idan ya sami wani mukami a gwamnati musamman na fannin magana da yawun gwamnati kasancewar mutum bashi da wata magana da ya isa ya yi sai da sahalewar gwamnati.
You must be logged in to post a comment Login