Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Ganduje zai yi wa ‘yan takarar kananan hukumomi gwajin ta’ammali da miyagun kwayoyi 

Published

on

Gwamnatin jihar Kano za ta tabbatar da yiwa  ‘yan takarar da za su tsaya zaben kananan hukumomi  gwajin ko suna ta’ammali da miyagun kwayoyi kafin gudanar da zaben shugabanin kananan hukumomi  a badi.

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan yau Talata wanda ya samu wakilcin Kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo a wajen taron wayar da kan ma’aikatan kananan hukumomi kan hanyoyin dakile sha da safarar miyagun kwayoyi.

Murtala Sule Garo ya ce nan gaba kadan gwamnatin Kano zata yi hadin gwiwa da hukumar hana sha da fataucin migayagun kwayoyi ta kasa reshen jihar Kano NDLEA wajen yi wa dukkannin ma’aikatan gwamnati gwajin ko suna ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Wakilin mu Abba Isa Muyhammad ya rawaito cewa daga cikin wadanda suka halacci taron akwai ma’aikatan kananan hukumomi da kuma masu ruwa da tsaki.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!