Labarai
Shirya taron zumunci zai wanzar da zaman lafiya a ƙasa – Ɗan kadan Kano
Ɗan kadan Kano kuma Dan majen Gwandu Alhaji Bashir Ibrahim Muhammad ya buƙaci al’umma da su riƙi zumunci a matsayin abinda zai ƙara kyautata alaƙarsu da yan uwan su a duk inda suke.
Alhaji Bashir Ibrahim ya bayyana hakan a ranar Litinin, a wajen taron zuriyar Marigayi Moddibo Mahmud da kuma gabatar da littafin tarihin zuri’ar.
Ɗan kadan Kanon ya ce, kowacce zuri’a tana yin ƙarko ne a duk sanda ƴaƴan cikinta suka ɗauki matakan ingantata musamman ta hanyar shirya taruka.
“Muna sane da tarihin yadda kowacce zuriya ke fara da kaɗan, sai kuma ta bazu zuwa sassan duniya ta ci gaba da yaɗuwa ta hanyar hayayyafa”.
“Zuri’ar Moddibo ta zo Kano ne tun daga zamanin marigayi sarki Abdullahi Maje Karofi ga shi a yanzu zuriyar ta fara tattaro kanta ta hanyar bincike da tuntuɓa”.
Alhaji Bashir Ibrahim ya kuma ce, ta hanyar shirya taron dangi ne za a san yawan zuri’a kuma zumunci zai ƙara danko da kuma samun haɗin kani da zaman lafiya.
Taron ya samu halartar ɗaukacin ƴaƴa da jikoki daga sassa daban daban na ƙasar nan.
You must be logged in to post a comment Login