Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarrafa shara: za mu rika samun naira miliyan 50 zuwa 100 kowanne wata- Ganduje

Published

on

Gwamnatin jihar Kano za ta rika samun naira miliyan hamsin zuwa miliyan dari a kowanne wata da zarar ta fara sarrafa shara.

Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan yayin da yake mika daftarin kundin yarjejeniyar sarrafa sharar ga kamfanin mai zaman kan sa.

Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya ce, kamfanin zai yi aiki ne karkashin kulawar hukumar kwashe shara REMASAB don tabbatar da kamfanin ya gudanar da aikinsa kamar yadda aka kulla yarjejeniya.

Ya ce gwamnati ta bai wa kwamfanin motoci da sauran kayan aiki a matsayin aro wanda za su rika biyan naira miliyan hamsin zuwa dari a kowanne wata.

“ karkashin yarjejeniyar mun tsara za mu samar da gurare goma da za su samar da tasha wadda zata rika gwada gurbatar yanayi don magance matsalar’ a cewar Getso.

Da yake jawabi shugaban kamfanin Alhaji Bashir Namadina ya alkawarta yin aiki cikin gaskiya da rikon amana.

“za mu dauki ma’aikata kimanin dubu hudu da zarar mun fara aiki wanda za su kasance ‘yan asalin jihar Kano don magance zaman banza” inji Namadina.

Shugaban hukumar kwashe shara ta REMASAB Alhaji Abdullahi Mu’azu Gwarzo ya ce za su yi duk me yiwuwa wajen ganin an fara aikin yadda ya kamata don samarwa da gwamnati kudaden shiga.

“Dama aikin mu ne tabbatar da an tsaftace jihar Kano da kuma ganin an samar da dabarun da za su inganta shara ta hanyar sarrafata don samun kudi da sauran sinadarai”. A cewar Gwarzo.

Tun da fari dai gwamnatin ta kulla yarjejeniyar aiki da kamfanin sarrafa shara mai zaman kan sa anan Kano wanda zai rika sarrafa shafar da jihar ke da ita wadda kuma yarjejeniyar zata dauki tsawon shekara 20 ana yin ta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!