Ƙetare
Shugaba Al-Burhan ya sanya ƙungiyoyin sa-kai da ke tallafawa a yaƙin Sudan cikin rundunar Soji

Shugaban gwamnatin Sojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan ya sanar da sanya ilahirin ƙungiyoyin sa-kai da ke tallafawa yaƙin ƙasar cikin rundunar Soji a wani yunƙuri na maye gurbinsu da mayaƙan RSF waɗanda a baya ke tallafawa wajen samar da tsaro a ƙasar.
Wata sanarwa da rundunar Sojin Sudan ta wallafa a shafinta na Facebook ta ruwaito cewa shugaba al-Burhan na umartar amfanin da tanadin dokar tsaro ta 2007 a ƙasar don sanya ilahirin masu taimakawa Sojojin waɗanda ke ɗauke da makamai a cikin rundunar.
Sanarwar ta nuna cewa daga yanzu rundunar Sojin Sudan ce za ta ci gaba da tafiyar da harkoki tare da sanya idanu kan dukkanin ƙungiyoyin mayaƙan da ke tallafa mata a yaƙinta da RSF.
A cewar rundunar wannan doka ta fara aiki daga ranar 16 ga watan Agustan 2025 wanda rundunar Sojin ta Sudan ta ce yunƙuri ne na dakile duk wata barazanar aikata ba dai- dai ba ta hanyar amfani da mayaƙan sa kai.
You must be logged in to post a comment Login