Kaduna
Shugaba Bola Tinubu yace babu dalilin da zaisa Najeriya jin tsoron matakan Trump

Shugaba Bola Ahmad Tinubu yace kudaden da kasar nan ke samu daga hanyoyin da bana man fetur ba sun isa wajen dakile tasirin manufofin tattalin arzikin shugaban kasarAmurka, Donald Trump.
Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kungiyar Buhari wato “Buhari Organisation” karkashin jagorancin tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, TankoAlmakura, a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Yace Najeriya ta riga ta cimma burin samun kudadenta na shekarar 2024 tun daga watan Agusta.
Shugaban yakara da cewa, Najeriya ta riga ta samu kudin da ta ke bukata a 2025 tun a watan Agusta.
Trump, ya sanya sabbin dokoki, ciki har da haraji masu tsauri wanda suka jawo suka daga sassa daban-daban na
duniya.
You must be logged in to post a comment Login