Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin bude iyakokin Nijeriya da Nijar

Published

on

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin sake buɗe kan iyakokin Nijeriya da jamhuriyar Nijar ta sama da ta ƙasa baki daya.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya fitar.

Sanarwar ta ce, shugaba Tinubu ya buƙaci a buɗe iyakokin ne nan take.

Haka kuma, Sanarwar ta ƙara da cewa shugaban ya ɗauki matakin ne sakamakon taron ƙoli na kungiyar ECOWAS da aka gudanar ranar 24 ga watan jiya na Fabrairu a birnin tarayya Abuja, inda shugabannin suka amince da ɗage takunkuman tattalin arziki da aka kakaba wa wasu ƙasashen ƙungiyar, ciki har da jamhuriyar Nijar.

Ana sa ran ɗage takunkumin zai rage zaman ɗar-dar da bunƙasa harkokin kasuwanci da tattalin arziki tsakanin Najeriya da ƙasashen da ke makwabtaka da ita.

Daga cikin takunkuman da aka ɗage sun hada da “Buɗe iyakokin ƙasa da na sama tsakanin ƙasashen biyu, da kuma na hana zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci da ke shiga da kuma fita daga Nijar.”

Haka kuma Najeriya ta sanar da ɗage takunkumin hana bai wa Jamhuriyar Nijar wutar lantarki da a baya ta yi.

“An kuma ɗage dokar hana hada-hadar kasuwanci da hada-hadar kuɗi tsakanin Najeriya da Nijar, tare da riƙe kadarorin ƙasar Nijar da ke babban bankin ECOWAS da kuma bankunan kasuwanci.” a cewar sanarwar.

Bugu da ƙari, umarnin na shugaba Tinubu ya ƙunshi ɗage dokar hana zirga-zirga da aka sanya wa jami’an gwamnati da ƴan’uwansu daga Nijar.

Haka kuma, matakin ɗage takunkumin kuɗi da tattalin arziki da aka ƙaƙaba wa Jamhuriyar Guinea ya nuna goyon bayan Najeriya ga ƙoƙarin daidaitawa da dawo da zaman lafiya a yankin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!