Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu ƙara kasafin kuɗi don biyawa ma’aikatan lafiya kuɗaɗen su – FG

Published

on

Gwamnatin tarayya ta yabawa ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta ƙasa NARD bisa janye yajin aikin sama da watanni biyu da suka yi.

Ministan ƙwadago da samar da aikin yi Chris Ngige ne ya bayyana lokacin da ya karɓi bakuncin shugabannin ƙungiyar ta NARD.

Chris Ngige ya yabawa shugaban ƙungiyar Godiya Ishaya bis ayadda ya umarci ƴaƴan ƙungiyar kan su koma bakin aikin su.

Kazalika ya bayyana musu cewa gwamnatin tarayya za ta ƙara kuɗaɗe a kasafin kuɗin baɗi don warewa ma’aikatan lafiya alawus-alawus da ya kai naira biliyan 47 daga 40 da ta ke biyna su kowacce shekara.

Sannan za a ci gaba da tura ma’aikatan lafiya domin samo horo da kuma biyan ma’aikatan kuɗaɗen alawus na haɗarin aikin corona.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!