Labarai
Shugaba Buhari ya amince da shawarwarin kwamitin yarjejeniyar kasuwanci
Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya amince da shawarwarin da kwamitin shugaban kasa ya ba shi dangane da shirin yarjejeniyar kasuwanci ba tare da shinge ba a nahiyar Afirka.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu, ya shaida cewa shugaba Buhari zai sanya hannu kan mataki na farko na yarjejeniyar da zarar ya halarci babban taron shugabannin nahiyar Afirka.
Taron wanda za a gudanar a birnin Niamey na Jamhuriyar Nijar nan da ‘yan kwanaki, shi ne taro na 12 kan batun kasuwanci ba tare da shinge ba ga kasashen nahiyar Afirka.
Yayin amincewa da shawarwarin kwamitin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana a fili cewa kasar nan za ta tabbatar da cewa an samar da manufofin da za su ci gaba da tallata kayayyakin da ake sarrafawa a Afirka don kara bunkasa tattalin arzikin nahiyar.