Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugaba Buhari ya bar birnin tarayya Abuja zuwa mahaifar sa Daura

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar babban birnin tarayya Abuja zuwa mahaifar sa Daura a jihar Katsina don gudanar da bikin babbar Sallah na bana.

Shugaba Buhari ya dawo babban birnin tarayya Abuja daga birnin London a ranar Asabar din da ta gabata bayan shafe kwanaki 10 a can, kuma ya tafi birnin Daura ne don gudanar da bukukuwan sallah.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar fadar shugaban kasa da ke Abuja zuwa Dauran ne da misalin karfe 3 da minti 6 na ranar yau Litinin.

Kafin tafiyar ta sa Shugaba Buhari ya jagoranci wani taro da shugabannin hafsoshin tsaron kasar nan a fadar shugabancin kasa dake villa a Abuja.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!