Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Shugaba Buhari ya bukaci a sake nazartar matakan karin wa’adin shugabanci jam’iyyar APC

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci shugabannin jam’iyya mai mulki da ta sake nazartar matakan da zai baiwa dukkanin shugabannin jam’iyyar karin wa’adin shugabanci jam’iyyar ta APC.

Shugaba Buhari ya kuma bukaci mambobin jam’iyyar da su nesanta kawunan su daga duk wasu daukar matakai da zai sanya jam’iyyun adawa su rika musu shagube.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne, lokacin da yake jawabi yayin taron majalisar zartaswar jam’iyyar ta APC a fadar shugabancin kasa ta Villa da ke Abuja a Talatar nan.

A cewar sa karawa shugabannin jam’iyyar wa’adin ba zai sabawa dokokin jam’iyyar ba, kamar yadda hakan yake a kundin tsarin mulkin kasar nan, tare da cewa ya samu shawarwarin shari’a daga Antoni Janar kuma ministan shari’ar kasar nan kan wannan batu.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!