Labarai
Shugaba Buhari ya bukaci gudunmuwar bankin musulunci don bunkasa rayuwa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci gudunmawar bankin raya kasashen musulmi (IDB) wajen bunkasa bangaren samar da abubuwan more rayuwa a kasar nan.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar..
A cewar Femi Adesina ta cikin sanarwar, shugaba Buhari, ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke ganawa da mataimakin shugaban bankin raya kasashen musulmi Dr. Mansur Mukhtar, a gefen taron kungiyar kasashen Afurka (AU) da ke gudana a birnin Yamai babban birniN Jamhuriyar Nijar.
Shugaba Buhari ta cikin snaarwar dai, ya kuma ce, yayin da adadin al’ummar kasar nan ke karuwa ba kakkautawa, akwai bukatar kara adadin kudaden da ake kashewa wajen samar da abubuwan more rayuwa.
Sanarwar ta kuma ruwaito, mataimakin shugaban bankin raya kasashen musulmi na duniya Dr. Mansur Mukhtar, na cewa, bankin zai ci gaba da bada gudunmawa wajen samar da abubuwan more rayuwa ga al’ummar Najeriya.
Yayin da a bangare guda, ya ce, nan ba da dadewa ba, shugaban bankin raya kasashen musulmin zai kawo ziyara Najeriya domin bude reshen ofishin bankin a kasar nan.