Labarai
Shugaba Buhari ya bukaci kasashen da aka ajiye kudin sata da su gaggaua dawo da su
Shugban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci kasashen da ake sace kudi a kai ajiya wajensu su gaggauta sakin kudaden ga kasashen da aka sato daga cikinsu cikin gaggawa ba tare da wani bata lokaci ba.
Shugaban kasar na fadin hakan yayin gabatar da jawabi a taron kasashen Afirka na bana a birnin Nouakchott da ke kasar Mauritania, wanda aka yi wa taken samun nasara kan yaki da cin hanci da rashawa, hanya daya da nahiyar Afirka da ta samu ci gaba mai dorewa.
Gabanin fara muhara kan yadda za a lalubo hanyar magance matsalar cin hanci da rashawa a Afirka, saida shugaba Muhammadu Buhari ya yi jawabin irin matakan da yake dauka domin kawar da matsalar a Najeriya.
Muhammadu Buhari ya ce nan gaba kadan zai shirya taron matasan Afirka a birnin tarayya Abuja, tare da hadin gwiwar shugaban kungiyar hadin kan Afirka AU Paul Kagame, wanda kuma shi ne shugaban Rwanda, domin tattauna yadda wakilcin Afirka zai kasance yayin babban taron Majalisar dinkin Duniya mai zuwa.
Har ila yau ya bayyana cewa babban taron da aka gudanar a kasar nan cikin watan Afrilun da ya gabata kan al’amuran tsaro da zaman lafiya, ya nuna karara irin illar da cin hanci da rashawa ke yi wa Afirka, a don haka ya bukaci hadin sauran shugabannin Afirka don ganin an magance matsalar.