Connect with us

Kiwon Lafiya

Shugaba Buhari ya mika ta’azziyar sa ga iyalan farfesa Sophie Oluwale

Published

on

Shugaban kasa Buhari ya aike da ta’azziyar sag a ‘yan uwa da iyalan marigayiya farfesa Sophie Oluwole mai aziki kuma mace ta farko da ta sami digiri na 3 kan ilimin falsafa a kasar nan.

Farfesa Sophie Oluwole ta rasu ne a ranar Lahadin da ya gabata a gidan ta dake Ibafo dake jihar Ogun tana da shekaru 83.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da mashawarcin shugaban kasa kan kafafan yada labarai Femi Adesina ya fitar cewa shugaban ya nuna alhinin sa bisa rashin farfesar a bangaren falsafa, yana mai cewar a Najeriya ta yi babbar rashi.

Muhammadu Buhari ya kara da cewar, bangaren ilimin falsafa ya samu nakasu ganin yadda marigayiyar ke bada gudunmawa a Najeriya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,340 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!