Connect with us

Kiwon Lafiya

Shugaba Buhari ya nuna alhininsa bisa rasuwar daliban jihar Bauschi

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna alhininsa bisa ga rasuwar daliban nan ‘yan asalin jihar Bauchi sama da ashirin sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa da su  jiya anan jihar Kano.

Shugaban kasar ya kuma jajantawa al’ummar garin Misau da jihar Bauchi dama kasa baki daya bisa ga rasuwar daliban, wanda ya ce babban rashi ne ga kasa baki daya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu ya fitar a Abuja.

Sanarwar ta kuma ruwaito shugaban kasar na addu’ar All.. ya jikan su ya kuma bai wa iyalan su hakurin jure rashi.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,677 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!