Connect with us

Kiwon Lafiya

An yi jana’izar daliban da suka rasa rayukansu a wani hatsari a jihar Kano

Published

on

Da maraicen jiya ne aka gudanar da jana’izar daliban nan ashirin da daya da malaman su uku wadanda suka rasa rayukan su a wani hatsarin mota da ya ritsa da su a yankin karamar hukumar Gaya da ke nan jihar Kano.

 

Rahotanni sun ce an gudanar da jana’izar daliban ne a fadar Sarkin Misau da ke garin na Misau a jihar Bauchi.

 

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa dubban mutane ne suka halarci jana’izar wanda limamin babban masallacin juma’a na garin Misau Sheikh Usman Baba ya jagoranta.

 

Daliban dai sun rasa rayukansu ne a jiya sakamakon wani mummunar hatsarin mota da ya ritsa da su a yankin karamar hukumar Gaya lokacin da suke komawa gida bayan kammala wata ziyarar karin ilimi da suka kawo nan jihar Kano wato Excursion.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,834 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!