Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugaba Buhari zai kai ziyara kasar Saudiyya

Published

on

A yau Talata ne ake saran Shugaba kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Saudiyya a wata ziyara ta karshe da zai kai wata kasar waje a matsayin shugaban kasa.

Shugaban zai shafe kusan mako guda, inda ake saran zai dawo gida Najeriya a ranar  19 ga watan Afrilun da muke ciki.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa kan kafafen yada labarai malam Garba Shehu ya fitar, ya ce, Shugaba Muhammadu Buhari zai kuma gudanar da aikin Umrah yayin ziyarar tasa.

Sanarwar ta kuma ce Shugaba Buhari zai samu rakiyar manyan mukarraban gwamnatinsa a wannan ziyara zuwa kasar Saudiyya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!