Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Ƙetare

Shugaba Macky Sall ya umarci yan sanda su dauki mataki kan zanga-zangar magoya bayan Ousmane Sonko

Published

on

Shugaban ƙasar Senegal Macky Sall ya  bai wa ƴan sanda umarnin daukar matakan da suka dace domin ganin an samar da tsaro, bayan mummunar zanga-zanga da magoya bayan madugun ƴan adawa Ousmane Sonko ke ci gaba da yi kan shari’ar da ake yi masa.

Mutum ɗaya ne ya rasa ransa a artabun tsakanin magoya bayan mista Sonko da kuma ƴan sanda.

Rahotonni sun bayyana cewa,an yi ta yin zanga-zanga a birane da ke faɗin ƙasar kan shari’ar da ake yi wa Sonko kan zargin ɓata sunan ministan yawon buɗe idanu wanda mamba ne a jam’iyyar mista Sall.

Sai dai Mista Sonko ya ce, ana yi masa shari’ar ne kawai don hana shi tsayawa takarar kujerar shugaban ƙasa a zaɓen  badi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!