Labarai
Shugaba Tinubu ya amince da biyan bashin wutar lantarki har tiriliyan 3.3

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya amince da wani shiri na biyan bashin wutar lantarki da ya kai naira tiriliyan 3.3, domin gyara matsalolin da suka dade suna addabar bangaren wutar lantarki a fadin Najeriya.
Ta cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar, gwamnatin ta ce, bashin ya samo asali ne tun daga shekarar 2015 zuwa 2025.
Tuni dai aka fara aiwatar da shirin, inda kamfanonin samar da wuta 15 suka rattaba hannu kan yarjejeniyar karɓar kusan naira tiriliyan 2.3, yayin da gwamnati ta ware sama da naira biliyan 500 domin fara biyan bashin.
You must be logged in to post a comment Login