Labarai
Shugaba Tinubu ya amince da biyan bashin wutar lantarki na Naira Tiriliyan 3.3

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya amince da wani shiri na biyan bashin wutar lantarki da ya kai naira tiriliyan 3.3, domin gyara matsalolin da suka dade suna addabar bangaren wutar lantarki a ƙasar.
ta cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya fitar, gwamnatin ta ce bashin ya samo asali ne tun daga shekarar 2015 zuwa 2025, kuma an cimma matsaya cewa za a biya shi gaba ɗaya.
Tuni dai aka fara aiwatar da shirin, inda kamfanonin samar da wuta 15 suka rattaba hannu kan yarjejeniyar karɓar kusan naira tiriliyan 2.3, yayin da gwamnati ta ware sama da naira biliyan 500 domin fara biyan bashin.
You must be logged in to post a comment Login