Labarai
Shugaba Tinubu ya bada umarnin bada horo da makamai ga jami’an tsaron Dazuka

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bada umarni ga mai bada shawara kan harkokin Tsaro na ƙasar nan, Malam Nuhu Ribadu, da ya tabbatar da an kammala bada horo tare da samar da makamai ga ƙarin jami’an tsaron Dazuka, wato Forest Guard nan da dan wani lokaci ba dadewa ba.
Umarnin na shugaban kasa na a matsayin mataki na ƙarfafa yaki da garkuwa da mutane da kuma ayyukan ta’addanci a faɗin kasar nan.
Tinubu ya ce wannan mataki na daga cikin muhimman shirye-shiryen gwamnatin sa na dawo da kwanciyar hankali musamman a yankunan da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da wasu laifukan da bata gari ke aikatawa a fadin kasar.
You must be logged in to post a comment Login