Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu ya bada umarnin dakatar da tsarin biyan kuɗi ta na’ura filayen jiragin sama

Published

on

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, tare da Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama FAAN, da su dakatar da aiwatar da tsarin biyan kuɗi ba tare da tsabar kuɗi ba a dukkan filayen jiragen sama na  nan take.

 

Matakin na zuwa ne bayan yawaitar koke-koken fasinjoji kan jinkiri da cunkoso da sabon tsarin ya haifar, lamarin da ya haddasa tsaiko a ayyukan filayen jirage tare da barin mutane da dama makale ba su iya kammala biyan kuɗaɗen su.

 

Rahotanni sun nuna cewa matsalolin na’ura da tangarɗar biyan kuɗi ta yanar gizo sun jawo tsaiko mai yawa, wanda ya haddasa rikice-rikice da ɓata lokaci ga matafiya.

 

Gwamnatin tarayya ta ce dakatarwar na wucin gadi ce, domin a sake duba tsarin yadda za a inganta shi ba tare da kawo cikas ga zirga-zirgar fasinjoji ba, tare da dawo da tsari da sauƙaƙa harkokin sufuri a filayen jiragen sama.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!