Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Akwai yiwuwar bude sauran filayen jiragen saman kasar nan- Hadi Sirika

Published

on

Gwamantin tarayya ta ce zata duba yiwuwar bude sauran filayen jiragen sama guda hudu dake jahohin kasar nan matukar za su yi biyayya ga dokokin da aka sharadanta na yaki cutar Corona.

Ministan harkokin sufurin jiragen saman kasar na Hadi Sirika ne ya bayyana hakan lokacin da ya ke bayani ga kwamitin yaki da cutar corona na gwamnatin tarayya jiya a Abuja.

Hadi Sirika ya ce a yau juma’a ne ake sa ran kai ziyarar duba yiwuwar bude filayen jiragen da ke Calabar da Sokoto da Katsina da kuma jihar Kebbi.

Ya kara da cewa a ranar ashirin ga watan Yulin da muke ciki ne filayen jiragen za su ci gaba da gudanar da ayyukan su bisa tsarin da aka gindaya musu.

Hadi Sirika ya kuma ce kowanne filin jirgi zai ci gaba da gudanar da ayyukan sa na yau da kullum karkashin ka’idoji da dokokin yaki da cutar corona kamar yadda hukumomin lafiya ke bada shawara.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!