Labarai
Shugaba Tinubu ya bada Umarnin raba shinkafa ga masu Azumi

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin a rarraba shinkafa ga al’ummar kasar nan da ke azumtar Ramadan da na Lent.
Kungiyar da ke goyon bayan siyasar Shugaban Tinubu, ta ce ta samu umarni daga shugaban kasar na ta raba shinkafa a fadin kasar domin tallafa wa ‘yan kasa da ke gudanar da azumin Ramadan da kuma azumin Kirista na Lent.
Darakta Janar na kungiyar Renewed Hope Ambassadors kuma gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, a baya baya nan wadda aka raba wa manema labarai.
You must be logged in to post a comment Login