Labarai
Shugaba Tinubu ya dawo Najeriya

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya dawo gida Najeriya bayan da ya kammala ziyarar aiki ta kusan makonni uku a nahiyar Turai, inda ya gudanar da muhawara da manyan jami’an kasa da kasa don inganta dangantaka tsakaninsu Najeriya a fannin tsaro da ci gaban tattalin arziki.
Jirgin shugaban ya sauka ne a filin Jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a daren ranar Litinin, inda ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnati ciki har da sakataren gwamnatin tarayya Sanata George Akume da shugaban Ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila da Mai ba da shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu da Ministan Kasafin Kudi da tsare-tsare Sanata Atiku Bagudu da ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike.
Idan za a iya tunawa tun a ranar 2 ga watan Afurilu ne shugaba Tinubu ya tafi Faransa inda daga can kuma ya zarce Birtaniya.
You must be logged in to post a comment Login