Labarai
Shugaba Tinubu ya gana da Gwamnan Kaduna Uba Sani

Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya gana da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Fadarsa da ke Abuja a ranar Juma’a, inda suka tattauna batutuwan tsaro, manyan ayyukan more rayuwa, da muhimman tsare-tsaren ci gaban Jihar Kaduna.
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar bayan ganawar.
A cewar sanarwar, gwamnan ya sanar da Shugaban Ƙasa dawowar masu ibada da aka sace daga coci-coci a garin Kurmin Wali da ke Karamar Hukumar Kajuru.
Gwamnan ya ƙara da cewa ganawar ta kuma tattauna kan fara aikin hanyar Birnin Gwari, da kuma muhimmancin gyaran hanyoyin Kaduna Eastern Bypass, Jere zuwa Kwoi zuwa Kafanchan, da Zaria zuwa Pambegua zuwa Saminaka, a matsayin muhimman hanyoyin zirga-zirga da ci gaban tattalin arziki.
Uba Sani ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki tare da Gwamnatin Tarayya wajen inganta tsaro da bunƙasa manyan ayyukan more rayuwa a faɗin Jihar Kaduna.
You must be logged in to post a comment Login