Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamna Uba Sani ya bayyana damuwa kan yaran da ba sa zuwa makaranta

Published

on

Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani, ya bayyana damuwarsa dangane da yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta a fadin jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da shugaban hukumar ilmi matakin farko ta jihar Kaduna bayan da ya gayyace shi ofishinsa domin tattaunawa game da matsalar rashin zuwan yaran makaranta.

Ta cikin jawabin da sakataren yada labaran gwamnan Muhammad Lawal Shehu, ya fitar, ta ce, gwamna Uba Sani, ya bayyana matukar damuwa bisa yadda adadin yaran da ba sa zuwa makarantar ke kara yawaita a jihar.

Gwamna Uba Sani, ya kuma yi kira ga hukumomin da ke da ruwa da tsaki da su kara zage damtse wajen kawo karshen matsalar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!