Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu ya jajanta wa ƴan kasuwar Singa bisa iftila’in Gobara

Published

on

Shugaban kasa Bola Tinubu ya jajanta wa ƴan kasuwar da suka tafka asarar miliyoyin naira da dukiyoyi bayan tashin gobara a Kasuwar Singa da ke jihar Kano.

 

Gobarar ta tashi ne da yammacin Asabar amma har safiyar Lahadi wuta na ci, lamarin da ya janyo mummunan asara a kasuwar.

 

Shugaba Tinubu – wanda ya nemi Gwamna Abba ya tattara bayanai kan gobarar – ya bayyana lamarin tamkar mummunan bala’i.

 

Haka kuma shugaban ƙasar ya nuna damuwarsa musamman kasancewar a mako biyu da suka gabata ma an samu gobara a kasuwar da ta lalata gomman shaguna da dukiyoyi.

 

Don haka ne ya nemi a gudanar da cikakken bincike kan dalilan de ke haifar da gobara a kasuwanni, lamarin da ke jefa ƴan kasuwa cikin mummunar asara da damuwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!