Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu ya musanta zargin da ake masa na ƙoƙarin mayar da Najeriya tsarin jam’iyya ɗaya

Published

on

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya musanta zargin cewa gwamnatin sa na ƙoƙarin mayar da kasar nan a tsarin jam’iyya ɗaya ko raunana jam’iyyun adawa. 

 

Shugaba Tinubu, ya musanta haka ne yayin da ya ke jawabi a wani taron shan ruwa a fadar shugaban Ƙasa da ke birnin tarayya  Abuja.

 

Ya ce, kalubalen tsaro kamar ta’addanci da fashi da makami na bukatar haɗin kan kasa maimakon rabuwar kan siyasa. 

 

Shugaban ya kuma bukaci al’ummar Najeriya da su bi tafarkin dimokuraɗiyya da magabata suka shimfiɗa, ya na mai cewa babu laifi idan wasu ‘yan siyasa sun sauya sheƙa, amma hakan ba ya nufin mayar da siyasar Najeriay kan tafarkin jam’iyya guda ɗaya ba ne.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!