Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Atiku Abubakar ya yabawa Bola Tinubu kan binciken masu almundahana

Published

on

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa ‘akwai wasu masu hannu a badaƙalar almundahanar kuɗi da ake zargin ministar jin ƙai, Betta Edu ta aikata’.

Atiku wanda ya yi takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jamiyyar adawa ta PDP a Zaben 2023, ya bayyana hakan yayin da yake yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan matakin da ya dauka na dakatar da ministar jin ƙan, duk da a cewarsa hakan ma kaɗai bai wadatar ba.

A ranar Litinin din da ta gabata ne Shugaba Tinubu ya dakatar da ministar, inda kuma ya umarci hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa ta gudanar da bincike a kanta.

Matakin na zuwa ne bayan ya fuskanci kiraye-kirayen ɗaukar mataki a kanta saboda zarge-zargen tafka almundahana, wanda ministar ta musanta.

Cikin wata wasiƙar martani da wani mataimakinsa na musamman Phrank Shaibu ya fitar, Atiku ya ce ‘abin takaici ne ganin yadda shirin da aka kafa da zummar tsamo ’yan Najeriya miliyan 100 daga matsanancin talauci amma kamar yadda ake zargi ya zama saniyar tatsa ga gwamnatocin jam’iyyar APC’.

Ya Kara da cewa, “Ko da yake Tinubu ya l ma’aikata. Sai dai Tinubu ya fifita siyasa a kan ƙwarewa, lamarin da ya janyo wannan abin kunya”

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!