Labarai
Shugaba Tinubu ya rantsar da Christopher Musa a matsayin Ministan tsaron

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya rantsar da Janar Christopher Musa a matsayin sabon ministan tsaro bayan amincewar majalisar Dattawa.
An yi bikin rantsar da tsohon babban hafsan tsaron kasar ne a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Villa, a birnin tarayya Abuja ranar Alhamis, kwana ɗaya bayan ‘yan majalisar dattawan sun shafe kusan awa biyar suna yi masa tambayoyi yayin tantance shi.
Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya wallafa hoton bikin rantsuwar a shafinsa na dandalin X, da ya tabbatar da lamarin.
You must be logged in to post a comment Login