Labarai
Shugaba Tinubu ya rantsar da kwamitin aikin Kidaya

Shugaban kasa Bola Tinubu, ya rantsar da kwamatin da zai tsara yadda za a gudanar da kidayar jama’a.
Shugaban, wanda shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ya wakilta ya bai wa ‘yan kwamatin wa’adin mako uku da su gabatar da rahotonsu.
Wata sanarwa da mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce Tinubu ya alakanta kidayar da abinda ke kawo ci gaban kasa.
Rahotonni sun bayyana cewa, Karo na karshe da Najeriya ta yi kidaya shi ne a shekarar 2006, inda kididdigar ta nuna cewa akwai mutane 140,431,790, yan asalin Najeriya da suka kunshi maza 71,345,488 da kuma mata 69,086,302.
You must be logged in to post a comment Login