Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu fara kidayar jama’a rana 29 ga watan Maris

Published

on

Hukumar kidaya ta Najeriya NPC ta ce, za a gudanar da kidayar jama’a daga ranar 29 ga watan Maris zuwa 2 ga watan Afrilun shekarar da muke ciki.

Shugaban hukumar Nasir Kwarra ne ya bayyana hakan a jiya juma’a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawarsa da shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kwarra ya yi alkawarin cewa aikin kidayar a bana zai sha bamban da na baya domin za a gudanar da shi ne ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Ya kuma bayyana cewa tuni hukumar ta kammala daukar ma’aikatan wucin gadi kuma an kammala tantance wuraren da aka yi kidayar gwaji a dukkanin kananan hukumomi 774, gabanin atisayen da za a kammala a ranar 2 ga watan Afrilu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!