Labarai
Shugaba Tinubu ya sauka a birnin Rome

Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya isa birnin Rome na ƙasar Italiya domin halartar taron shugabanni na Aqaba Process, wanda zai tattauna kan batutuwan tsaro a yankin Yammacin Afirka.
Taron wanda aka assasa tun a shekarar 2015 na Sarki Abdullah II na Jordan tare da haɗin gwiwar Italiya, zai mayar da hankali kan yaduwar ta’addanci a yankin Sahel, laifukan da ke da alaka da ruwa a gabar tekun Guinea, da kuma tsattsauran ra’ayi ta kafafen intanet.
Tinubu zai yi ganawa ta musamman da wasu shugabanni don samar da hanyoyin magance matsalolin tsaro a nahiyar Afrika.
Yayin tafiyar tasa Shugaba Tinubu ya samu rakiyar manyan jami’an gwamnati ciki har da Ministan Harkokin Waje Bianca Odumegwu–Ojukwu, Ministan Tsaro Mohammed Badaru, da Mai ba da shawara kan tsaro Nuhu Ribadu.
You must be logged in to post a comment Login