Labarai
Shugaban Ƴan kasuwar Kwari ya musanta sayar da ofishin yan kwana-kwana

Shugaban gammayar ƙungiyoyin ƴan kasuwar Kantin Kwari Musa Umar Sanda Arzai, ya ce maganar cefanar da ofishin jami’an kashe gobara na kasuwar ba gaskiya bane biyo bayan zargin da yan kasuwar suka yi dake cewa, an sayar da ofishin har ma an fara gine shi.
Musa Umar Sanda Arzai ya bayyana hakan ne yayi zantawa da manema labarai a kasuwar ta kantin kwari.
Ya kuma kara da cewa hakan biyo bayan korafe-korafen da suka yita samu kan ana yin abubuwan da basu dace ba a wajen yasa hukumar kasuwar da ammincewarsu daukar wannan matakin.
Haka kuma ya bayyana cewa, sun karbi koken yan kasuwar kan harajin da suka ce an tsawwala musu, inda ya ce za su bibiyi batun tare da ɗaukar matakan da suka dace.
Shugaban ya kuma bukaci yan kasuwar da su kwantar da hankulansu domin kuwa, kungiya za ta yi duk abinda ya dace domin daidaita komai a kasuwar.
You must be logged in to post a comment Login