Labarai
Shugaban Bola Tinubu ya gana da Gwamnonin jam’iyyar APC

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi wata ganawar sirri da Gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki a fadar shugaban kasa da ke Abuja a daren ranar Laraba.
An gudanar da wannan ganawa ne sa’o’i kadan kafin babban taron Kwamitin Zartarwa na kasa na jam’iyyar wato NEC wanda za a yi a yau Alhamis.
Rahotonni sun bayyana cewa Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo, wanda ke jagorantar kungiyar Gwamnonin APC, ya jagoranci sauran gwamnoni zuwa fadar shugaban kasa, bayan sun kammala wata ganawa da suka yi a gidan gwamnatin jihar Imo da ke Asokoro a birnin tarayya Abuja.
jaridar Dialy Trust ta ruwaito cewa, ana sa ran ganawar za ta taimaka wajen cimma matsaya kan muhimman batutuwa kafin taron babban taron na jam’iyyar APC musamman batun mukamin Shugabancin Jam’iyyar na kasa, wanda ke ci gaba da haifar da ce-ce-ku-ce tun bayan saukar tsohon shugaban jam’iyyar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya yi murabus daga shugabancin APC a baya bayan nan.
You must be logged in to post a comment Login