Labarai
Shugaban hukumar EFCC ya farfaɗo bayan samun kulawar likitoci

Shugaban hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa EFCC ya Abdurasheed Bawa ya samu sauƙi tun bayan faɗuwa da yayi a fadar shugaban ƙasa.
Mai magana da yawun shugaban Wilson Uwuraren ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
Ya ce a yanzu haka likitoci sun tabbatar da Abdurrasheed Bawa ya farfaɗo cikin ƙoshin lafiya.
Wannan ya biyo bayan sa’o’i ƙaɗan da faɗuwar Abdurrasheed Bawa yayin da yake jawabi a fadar shugaba Buhari.
You must be logged in to post a comment Login