Connect with us

Labaran Kano

Shugaban hukumar tattara haraji na cikin gida a Kano ya yi murabus

Published

on

Labarin dake ishe mu a yanzu-yanzu na nuni da cewar, Shugaban hukumar tattara haraji na cikin gida Sani Abdukadir Dambo yayi murabus daga kan mukamin sa a yau Alhamis.

Wannan na dauke cikin sanarwar da shugaban hukumar ya aikewa ofishin sakataren Gwamnatin jihar Alhaji Usman Alhaji a dazun nan.

Sai sanarwar bata fayece dalilan da suka sanya shugaban hukumar ta tattara haraji na cikin gida Dambo ya sanya yayi murabus ba amma kuma ya godewa Gwamnatin jihar Kano da ta bas hi damar yin aiki cikin Gwamnatin sa.

Muna dauke da cikakken labarin a nan  gaba.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 332,922 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!