Labarai
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya cire sunayen wasu daga cikin mutanen da ya yi wa afuwa.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan takardun afuwar da ya yi ga wasu da aka yanke wa hukunci.
Bayan shawara da majalisar koli da ra’ayoyin jama’a, shugaban kasa ya sake duba jerin wadanda za a yi wa afuwa, inda ya cire wadanda suka aikata manyan laifuka kamar garkuwa da mutane, fataucin miyagun kwayoyi, da zamba.
Shugaban kasar ya ce matakin ya zama dole domin kare tsaro da kuma kula da hakkokin wadanda abin ya shafa. Ya kuma bada umarnin cewa nan gaba ofishin kwamiti mai ba da shawara kan afuwa zai koma karkashin ma’aikatar shari’a maimakon ma’aikatar ayyuka na musamman.
Haka kuma, ya umurci Attorney General na kasa da ya fitar da sabbin ka’idoji domin tabbatar da cewa duk wanda zai amfana da afuwa ya cika ka’idojin doka.
You must be logged in to post a comment Login